Wednesday, 18 April 2018

MUHIMMANCIN TAUSA WAJEN KWANTARWA DA TAYARWA 001

GABATARWA:

Assalamu alaikum wa Rahmatullahi wa barakatuhu.

Dukkanin godiya da yabo da yabawa, sun tabbata ga Allah, masani wanda ya sanya kauna da jin dadi da kyautatawa a tsakanin ma’aurata.

Tsira da amincinsa su tabbata ga Annabi Muhammad SAW da iyalansa da sahabbansa da sauran bayin Allah salihai har ranar lahira.

To, Alhamdulillah, muna godewa Allah a bisa dama da iko daya bamu na riskar wannan rana mai alkhairi, a wannan dakin taro mai albarka, a karkashin shiryawa da kulawar wannan cibiya ta bincike da koyarwa tare da wayarwa da mata kai ta DAKE AKE GLOBAL CONSULTANCY Allah ya qara sanya mana albarka da alkhair yasa dukkanin abubuwan da zamu fada su zama daidai a mizani na gaskiya da lafiya tare da neman ladanmu a wajen Allah.

Shi kuma kuskure dama dan Adam a cikinsa yake to idan har an ci karo dashi ayi min afuwa tare da roka min Allah gafararsa, ya hada mu a ladan gabadaya, nagode Allah yayi muku albarka.

Kamar yadda aka nemi da nayi bayani dangane da Muhimmancin Tausa wajen kwantar da sha’awa ko tayar da ita, in sha Allahu zanyi bakin bayanin abinda Allah subhanahu wa ta’ala ya sanar dani, kuma gwargwadon fahimtarku.

Abubuwan da suka gaza ambatuwa anan sai ayi hakuri, ko a tuntubemu a ofishin ita wannan cibiya dake zoo road, in sha Allah.

To, amma kafin mu kai ga sanin mahimmancin ita tausar, ya kamata mu fara da bayanin ita kanta tausar, kamar haka;

1. Mecece tausa?

2. Hanyoyin da ake gudanar da tausa

3. Muhimmancin ta ga jikin ɗan Adam

4. Waɗanda ba’a yi wa tausa.

5. Rabe-raben tausa

6. Kammalawa (conclusion)

SABODA ƘURACEWAR LOKACI ZAMU DAKATA ANAN, SAI WANI MAKON INDA ZAMU ƊORA DAGA INDA MUKA TSAYA IN SHA ALLAH.

DOMIN QARIN BAYANI ZAKU IYA TUNTUBARMU KO ZIYARTAR SHAFUKANMU NA SADARWA (Social media) A ADIRESHINMU DAKE KASA;

E-MAIL: info@dakeake.com

FACEBOOK PAGE: Dake Ake Global

INSTAGRAM: dakeake

TWITTER: dakeake

FARFAJIYAR DAKE AKE NA WHAT’SAPP: masu bukatar shiga wannan farfajiya zasu iya aikowa ta wadannan lambobi; 0812 222 8484, 0817 997 7373.

Hadiza Balanti
CEO
DAKE AKE GLOBAL CONSULTANCY
BN2399256 TIN19603064

18-April-2018M

#dakeake

https://www.dakeake.com