Thursday, 10 November 2016

DAKE AKE GLOBAL CONSULTANCY

*KO KIN SAN DAKE AKE GLOBAL CONSULTANCY?*

*Dake Ake* cibiya ce wacce malama Hadiza Balanti Chediyar 'yan gurasa ta qirqira (kafata), don samar da zaman lafiyar ma’aurata, gyara mu’amalar auratayya da taimakawa matan aure, da auren kansa da ma masu shirin yin auren a arewacin Nigeria.

Cibiyar *Dake Ake*ta kunshi masana kwararru kuma jajirtattu wadanda aikinsu shine samar da nutsuwa ga auren da bashi da ita, ko nutsar da zukatan ma’aurata ya zama aure ya amsa sunansa ba wai auren jeka nayi ka ba.

Wannan cibiya mai albarka ta *Dake Ake* tana horar da amare hanyoyin kyautata aure da dama, musamman sanin auren, yadda ake yinsa, yadda ake jinsa da kuma yadda ake samunsa. Wanda hakan zai taimaka matuka gaya don shafe manyan matsalolin da ka iya zama qashin bayan rashin samun gamsuwa a auren yanzu.

Cibiyar *Dake Ake* a shirye take domin taga ta farfado da auren daya suma ko yake kan gargara ko wanda aka shaqe ko ya hadu da mutuwar barin jiki. Har ila yau, wannan cibiya mai albarka ta *Dake Ake* tana kan bawa mata da maza ma’aurata rigakafin matsaloli da cututtukan da aure ka iya kamuwa dasu da yadda ake gane su, da hanyoyin warwarewa ko guje musu gabadaya, amma ga wadanda suka harbu da matsalolin akwai hanyoyi masu yawa na warkewa daga cutukan ta hanyar bada shawarwarin da suka dace ko koyar da dabarun iya zama da miji lafiya hayyan.

Bugu da kari, ga masu shirin yin auren (zawarawa da ‘yammata) akwai sashen da yake horar dasu tare da dora su akan turbar da ba zasu karkace ko lalace ko bace ba in sha Allah.

Cibiyar *Dake Ake Global Consultancy* tana aiwatar da abubuwa masu dimbin yawa a cikinta.

*Daga cikinsu akwai;*

*1.* Bada shawarwari ga ma’aurata na da dana yanzu, da makamantansu

*2.* Bayar da ilimi da horarwa da shawarwari ga amare ko angwaye ko zawarawa.

*3.* Gyaran jiki dan gaske, wanda yake sawa a gane wacece ke.

*4.* Musulmar kwalliya ga amare wacce bata hana sallah idan lokaci yayi.

*5.* Lallen amare ja da baki dana zaman gida.

*6.* Wanka da yadda ake yinsa a zamanance.

*7.* _FADAMAR QAMSHI_ a bangaren Turaren gyara mai haskakawa da bulbulo kyan ‘ya mace.

*8.* Sinadaran da ke tsabtace fata daga dukkan abin qi ga kalarki.

*9.* Kayan ado da kwalliya na mata (zobba, yari da sarka, agogon hannu da Sarkar hannu dss).

*10.* Kyan ado da gyaran daki tsab (kayan bacci, kananan kaya na ciki da waje).

*11.* Koyar da salon sace zuciyar miji, yi masa dabaibayi da farin zare (yanga, kissa, kisisina amma duka na halali).

*12.* Turarurruka (masu Magana da kurame da masu tayarwa da kwantarwa, tare da masu sanya kauna da bege ga miji).

*13.* Sinadaran gyara da waraka da na musamman (na cututtuka dana gyara tsaiwa da iya tafiya).

*14.* Wannan cibiya tana shirya tarurruka (seminar and workshop), shirya walima, yin nasihohi ga ma’aurata ko a wajen walimar aure ko ta suna, MC ko DJ, rubuta talla ko sanarwa, daukar bidiyo ko hotuna, yin talla ko tallata haja ko sanar da taro ko biki ko suna.

da dai makamantan wadannan in sha Allah.

*DOMIN QARIN BAYANI ZAKU IYA TUNTUBARMU KO ZIYARTARMU A ADIRESHINMU DAKE KASA* 👇🏻👇🏻👇🏻

*OFFICE ADDRESS:*  Shop No. 3, Plot 7 Upstairs, Opp MRS Filling Station, Near Ja'iz Pharmacy, (Adjacent to MTN Office Zoo Road Branch) Zoo Road, Kano.

*BANKER:* 022 5311 494 GTBANK, Zaria Road Branch, Kano.

*TELEPHONE:* 0812 222 8484 (call only), 0817 997 7373 (whatsapp only), 0803 888 9681 (text sms only).

*OPENING TIMES:* Saturday to Thursday: 11am - 4pm
Friday: off

*E-MAIL:* dakeake@gmail.com

*FB PAGE:* Dake Ake Global

*BLOGSITE:* http://dakeake.wordpress.com

No comments:

Post a Comment