DAKE AKE
Ina kallon rayuwa kamar tafiyar ababen hawa ne a kan titi, wasu a mota wasu a mashin wasu a keke wasu a kafa, wasu sun iya tuki wasu koyo suke, wadanda basu iya tsallaka titi ba a kadesu.
Wani yaja abin hawansa a guje, wasu kuma a tafe suke sannu-sannu kwana nesa.
Wani a inda ya tsaya, wani daga nan zai fara, wani ya mike wani yayi kwana, wani abin hawansa ya baci, shi ko wani man sa ya kare, wani ya rage wa wani hanya wani kuma babu mai rage masa, kowa ta kansa yake.
Gashi ba tsere ake ba!
Wani kusa zashi wani kuma nesa, wani yayi tuki a nutse ya isa lafia wani kuma yayi ta ganganci yayi hatsari.
Ya yar uwata ki kalli rayuwa ta wacce fuska zamu gane hikimominta da tsarinta a saukake?
0812 222 8484
https://www.facebook.com/dakeake
Fb.me/dakeakeglobal
dakeake@gmail.com
No comments:
Post a Comment