Saturday, 12 November 2016

MAGANIN KASUWA

*DAKE AKE*🌹

_wata baiwar Allah ce take tambayata kamar haka;_

*```...Don Allah malama wai shin menene sirrin nasarar dakeake...?```*

Sai kawai na bata wannan labarin na kasa👇🏻

*MAGANIN KASUWA!*

A cikin magabata akwai wani mutum da ake kiran sa Abu Ubaydin Al-Mardaawiy, ya kasance idan ya kasa kaya a kasuwa mutene suna *'tururuwa'* wajen siyan kayansa. Sai wani ya tambaye shi, ya ce: _"Malam, wai menene sirrin ne, mutene suke tururuwar siyan kayanka, bayan akwai irin su a ko'ina cikin kasuwa?_

Sai Abu Ubaydin ya ce: ```"Ni na dauki kasuwancina a matsayin sababin arziki na; ba wai gundarin arzikin ba, saboda haka na kasance:

1. Ina yin gaskiya a cikin kasuwanci na.

2. Ba na boye aibin abin siyarwata.

3. Ina hakuri da riba kadan.

4. Idan na ci riba, sai na gode wa Allah, ba na yin alfahari da dagawa.

5. Idan na yi asara sai na yi hakuri, ba na raki da kwarmato.

6. Ba na hassada da ganin kyashi ga abokin kasuwancina yayin da ya samu ciniki.

7. Ba na alfahari da gwalangwaso ga abokan kasuwancina don na yi ciniki, su ba su yi ba.

8. Hada-hadar kasuwanci na ba ya shagaltar da ni bisa ambaton Allah da sauke wajiban da ke kaina.

9. Ina yawaita sadaka cikin abin da na samu na riba.

10. Nakan yi farin ciki yayin da nake qidaya kudin da zan bayar zakka, sama da yarda nake farin ciki yayin da nake qidaya uwar kudina. (bi ma'ana: ina fitar da zakkata cikin farin ciki)```

Wanda ya yi tambayar sai ya ce: _"Da na gwada wadannan abubuwa, sai na zamo hamshakin dan kasuwa._

Abdullah Ar-Rahili, *"Al-Aqlaqu -Alfaadhilah"* shafi-212.

*KARIN BAYANI:*
Idan muka yi nazarin wadannan abubuwa guda 10 zamu ga kowane daya daga ciki, ba za'a rasa aya ko hadisi da yake tabbatar da shi ba.

*```ALLAH YA BA MU SA'A DA NASARA YA KAWO MANA CINIKI DA KASUWA MAI ALBARKA DA TARIN ALKHAIR.```*
#dakeake

DAKE AKE GLOBAL CONSULTANCY
*OFFICE ADDRESS:*  Shop No. 3, Plot 7 Upstairs, Opp MRS Filling Station, Near Jaa-eez Pharmacy & Stores (Adjacent to First Bank Zoo Road Branch), Zoo Road, Kano.

*BANKER:* 022 5311 494 GTBANK, Zaria Road Branch, Kano.

*TELEPHONE:* 0812 222 8484 (call only), 0817 997 7373 (whatsapp only), 0803 888 9681 (text sms only).

*OPENING TIMES:* Saturday to Thursday: 11am - 4pm
Friday: off

*E-MAIL:* dakeake@gmail.com

*FB PAGE:* Dake Ake Global

*BLOGSITE:* http://dakeake.blogspot.com

2 comments: